A yayin ziyarar da ya kai kasar Ukraine, Shugaban Turkiya Raceep Tayyip Erdogan ya ce, dole ne a kawo karshen yakin Rasha da Ukraine, yana mai cewa, a shirye ya ke ya shiga tsakani muddun hakan zai sa a dakatar da fadan da aka kwashi fiye da watanni biyar ana yi. Daga karshe Ukraine da Turkiyya sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar a ganawar ta birnin Lviv, inda Ankara ta shiga cikin shirin sake gina Ukraine bayan yakin. Hakazalika Shugaba Erdogan ya yi alkawarin sake tuntubar takwaransa na Rasha Vladimir Putin kan batun sulhu.
A daya bangaren, Shugaban Volodymyr Zelensky ya yaba da ziyarar da babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da Shugaba Recep Tayyip Erdogan, yana mai cewa ziyara ce mai matukar muhimmanci da kara masa kwarin gwiwa a yakin da kasarsa ke yi da Rasha. Zelensky ya kara jan hankalin bakin nasa, kan hana hare-haren Rasha kan cibiyar makamashin kasar wadda ita ce mafi girma a nahiyar Turai, wanda ake ganin wata babbar barazana ce ga tsaron duniya baki daya.