Ganawar Biden da Modi kan Ukraine

Ganawar Biden da Modi kan Ukraine
Shugaban Amirka Joe Biden ya yi kira ga shugaban Indiya Narendra Modi kada ya cigaba da sayen makamashin mai daga Rasha

Shugaban Amirka Joe Biden ya yi kira ga shugaban Indiya Narendra Modi kada ya cigaba da sayen makamashin mai daga Rasha yayin da Amirka da sauran kasashe suke kokarin toshe hanyoyin kudin shiga da Rasha ke samu sakamakon mamayar da ta yi wa Ukraine.

Sai dai kuma Firaministan India bai bada wani kudiri game da bukatar ba.

A ganawar da shugabannin biyu suka yi ta kafar bidiyo, Biden ya shaidawa Modi cewa Amirka za ta iya taimakawa Indiya fadada hanyoyin samun makamashi.

A wata ganawar ta daban tsakanin sakataren harkokin wajen Amirka Anthony Blinken da takwaransa na Indiya, Subrahmanyam Jaishankar ya ce kamata ya yi Amirka ta mayar da hankali akan kasashen Turai amma ba Indiya ba game da damuwa kan makamashi daga Rasha.

Matsayin Indiya na kin karkata ga kowane bangare a game da yakin ya haifar da damuwa ga Amirka matakin da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya yabawa Indiya yana mai cewa ta yi adalci ta kuma yi cikakken nazarin halin da ake ciki.
 


News Source:   DW (dw.com)