Gabon ta shigar da kara kotun ICJ kan wani tsibiri mai fetur

Gabon ta shigar da kara kotun duniya ta ICJ da ke birnin Hague, bayan ikirarin mallakar wasu tsibirai uku masu dinbin arzikin man fetur, tana mai cewar tun shekaru hamin da suka gabata ne aka warware takaddamar, tsakaninta da Equatorial Guinea, wato a shekarar 1974. Sai dai Equatorial Guinea ta yi watsi da wannan ikirari na Gabon, inda ta ce ba shi da tushe a hukumance.

Takaddamar ta samo asali ne tun sama da shekaru 120 da suka gabata, lokacin da 'yan mulkin mallaka wato Faransa da Spain suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar ikon tsibiran, wadanda ke da arzikin man fetur da iskar gas.


News Source:   DW (dw.com)