Shugaba Scholz ya sanar da hakan ne a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai gabanin taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G20.
Karin bayani: Zelensky na fatan kawo karshen yaki da Rasha a 2025
Shugaban ya kuma kare matsayarsa na bai wa Isra'ila tallafin makamai da kuma goyon baya inda yace Isra'ila na da damar kare kanta daga duk wata barazana duk da cewa matakin na Jamus na shan suka daga kasashe da dama.
Karin bayani: Joe Biden ya yi kira ga Jamus da ta kara tallafa wa Ukraine
Shugaban kasar Brazil Luiz InĂ¡cio Lula da Silva na son a tattauna batun yakin Ukraine a wajen taron na G20 duk da cewa bai aike da goron gayyata ga shugaban Volodymyr Zelensky na Ukraine ba, amma ya gayyaci Rasha inda Ministan Harkokin Waje Sergei Lavrov ke wakiltar kasar.