Sa'o'i kadan kafin rasuwarsa a ranar 31 ga watan Mayu na shekarar 2022, fitaccen mawakin ya yi waka a wani shagali a Nazrul Mancha, wani wuri a kwalejin Sir Gurudas Mahavidyalaya da ke birnin Kolkata na gabashin Indiya.
Marigayi Kunnath yana rikodin wakokinsa don amfani da su a fina-finai, aikin da ya sa shi shahara a kasar da ma sauran kasashen duniya, yayin da ya ba da muryarsa ga daruruwan fina-finan Bollywood. Marigayin ya yi fice bayan fitowar kundin wakokinsa na farko mai taken "Pal" a shekarar 1999.
Baya ga fitattun jaruman masana'antar da masu ruwa da tsaki a harkar, Firaiministan Indiya Narendra Modi ya aike da sakon ta'aziyya ga iayalan marigayin, inda yace "Abin bakin ciki da rasuwar fitaccen mawakin nan Krishnakumar Kunnath wanda aka fi sani da KK. Wakokinsa sun nuna sha'awa iri-iri wanda hakan ya sa mutane daban-daban suka mamaye shi. Za mu rika tunawa da shi ta hanyar wakokinsa."
Fitaccen jarumin fina-finan Indiya Akshay Kumar ya fada a shafinsa na twitter cewa, "Mai matukar bakin ciki da kaduwa da sanin bakin cikin rasuwar KK. Wannan babban rashi ne! Om Shanti."
Mai shirya fina-finai Vivek Agnihotri ya ce ya yi matukar bakin ciki da jin labarin mutuwar Kunnath, inda ya ce ya rera waka ta farko a fim dinsa na farko, kuma tun lokacin ya kasance
"Me yasa da wuri haka, KK, me yasa? Amma kun bar taska na lissafin waƙa. Dare mai wahala. Om Shanti. Masu fasaha kamar KK ba su mutu ba, "in ji Agnihotri.
Aikin farko na Kunnath a Bollywood shine wakar, "Tadap Tadap Ke" daga fim din, "Hum Dil De Chuke Sanam."
Sauran wakokinsa da suka shahara sun hada da "Sach Keh Raha Hai" daga cikin fim din "Rehnaa Hai Terre Dil Mein" da wakar "Mangalyam," na fim din, "Saathiya."
Dubban masoya marigayin sun yi ta nuna alhinin mutuwar ta hanyar wallafa hotunansa a shafukan sad azumunta lokacin da yake rewa wakoki a bainar jama'a.
An haifi marigayi Krishnakumar Kunnath a watan Agusta 1968 a birnin New Delhi, Kunnath ya gama karatu daga Kwalejin Kirori Mal na Jami'ar Delhi, kafin ya fara aikinsa ta hanyar rera wakokokin don tallace-tallace.
Masana'antar Bollywood ta yi asarar fitattun jarumai a ‘yan shekarun nan, ciki har da fitacciyar mawakiya Lata Mangeshkar mai shekara 92 a watan Fabrairu da fitaccen jarumi Dilip Kumar a shekarar 2021 wanda ya mutu yana da shekara 98.