Firaministan Sri Lanka ya yi murabus

Firaministan Sri Lanka ya yi murabus
Firaministan Sri Lanka Mahinda Rajapaksa ya yi murabus bayan zanga-zanga mai karfi da ta kaure lokacin da magoya bayansa dauke da sanduna da kulake suka kai wa masu zanga-zangar hari.

Jam'iyyar adawa mafi girma a kasar ta ce tun kafin rikicin, ba za ta shiga cikin gwamnatin da Rajapaksa ke jagoranta ba, sai dai murabus na Firayim Minista kai tsaye, yana nufin an rushe majalisar ministocin kasar.

A ranar Litinin ne rikici mafi girma ya kaure a kasar lokacin da magoya bayan iyalan Rajapaksa suka yi ta kai farmaki, 'yan sanda sun harba barkonon tsohuwa tare da fesa ruwan zafi. An kuma ayyana dokar ta baci nan take a garin Colombo wanda daga baya aka fadada har ya hada da daukacin tsibirin Kudancin Asiya mai mutane miliyan 22.

Kasar Sri Lanka ta yi fama da matsalar karancin abinci da magunguna da mai na tsawon watanni, matakin da ya kara gtsananta matsin tattalin arzikin da kasar ke ciki tun bayans amun 'yancin kai da karancin abinci da man fetur da magunguna a cikin mawuyacin halin da take ciki na tabarbarewar tattalin arziki tun bayan samun ‘yancin kai.


News Source:   DW (dw.com)