Firaministan Mauritius ya amince da shan kayin zaben kasar

Firaministan kasar Pravind Jugnauth ya amince da shan kayin da jam'iyyarsa ta Lepep Alliance ta yi, a zaben da aka gudanar ranar Lahadi, duk da cewa ba a kai ga sanar da kammalallen sakamakon zaben ba.

Sakamakon da ke fitowa ya nuna cewa jagoran adawa ta Alliance of Change Coalition Navin Ramgoolam ke kan gaba a zaben, inda yake kan hanyarsa ta sake zama firaminista a karo na uku a tarihi.

Karin bayani:Mauritius

Mr Jugnauth wanda ke jagorantar Mauritius tun a shekarar 2017, ya ce sakamakon zaben na nuni da zabin al'ummar kasa, kuma wajibi ne ya mutunta ra'ayinsu da bukatarsu, a don haka ne yake yi wa kasarsa da al'ummarta fatan alheri.

An sa ran sanar da cikakken sakamakon zaben cikin daren Litinin din nan ko kuma zuwa wayewar garin ranar Talata.


News Source:   DW (dw.com)