Da dama dai na ganin akwai sauran runa a kaba kan siyasar Johson din bayan da wasu da dama suka ki mara masa baya.
Yan majalisu 211 suka kada kuria goyon bayan firaministan yayin da 148 suka kad kuiar kin amincewa, a cikin jmilar yan majalisu 358
Firanministan ya bayyana sakamakon a mai mahimmanci da gamsarwa, ya na mai cewa a yanzu gwamnatinsa za ta cigaba kuma za ta mayar da hankali kan batutuwa masu mahimmanci.
Kuru'ar da aka kada dai na zuwa ne bayan an zarge shi da saba dokokin hana yaduwar corona, batun da ya rage masa farin jini a idon al'umma kana suke kallonsa a matsayin Firanministan Birtaniya na farko da ya taba saba doka.