Sabon Firaminita Fathi Bachagha da ke samun cikakken goyon bayan majalisar shu'ra ta gabashin kasar Libiya ya shiga babban birnin kasar ne tare da rakiyar wasu ministoci don fara aiki. Jim kadan bayan da aka bayyana shigar tawagar, rikici ya barke tsakanin mayakan sa kai da ke goyon bayan bangaren gwamnatin da na Firaminista Abdelhamid Dbeibah, da yanzu haka ke rike da maadafan iko.
Duk da turabukin da ya samu na zartar da harkokin mulki a Libiya, Fathi Bachagha ya kasa tafiyar da aikin gwamnati bisa kememen da hamshakin dan kasuwa kuma firaminista Abdelhamid Dbeibah ya yi na bayar da kai bori ya hau, bayan da majalisar ta shu'ra ta hakikance cewa ya kammala wa'adinsa na mulki.