Firaiministan Isra'ila na fuskantar barazana

Firaiministan Isra'ila na fuskantar barazana
Rundunar tsaron Isra'ila ta kara karfafa tsaro tun bayan da aka yi yunkurin halaka iyalan firaiminista Naftali Bennett har sau biyu a cikin mako guda.

Rahotannin sun tabbatar da shirin halaka iyalan Firaiminista Naftali Bennett da yanzu haka ke fuskantar barazanar kisa daga wasu da ba a iya tantancewa ba, rundunar tsaron kasar ta sheda hakan ne, bayan da aka tura masa wata wasika da aka sanya harsashin bindiga a cikinsa. Masu binciken sirri na zargin cewa, dan Firaiministan mai shekaru goma sha bakwai ake hari a baya-bayan nan.

Firaiminista Naftali ya fito ya gargadi 'yan kasar a game da munmunan tasirin da kasa ka iya fadawa ciki a sakamakon rarrabuwar kawuna bayan da ya koka da irin rikicin da ke gudana a tsakanin al'ummar kasar a yayin da yake jawabi ga 'yan kasa a lokacin taron tuni da kisan kiyashin da aka yi ma Yahudawan. 


News Source:   DW (dw.com)