A wannan Laraba majalisar dokokin kasar Finland ta bude muhawara kan shigar kasar kungiyar tsaro ta NATO ko OTAN, sakamakon kutsen da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine. Ita dai Finland tana cikin kasashen da ke makwabtaka da Rasha, kuma kasar ta Rasha ta sha nuna adawa kan shigar Finland kungiyar tsaron ta NATO.
A makon jiya Firaminista Sanna Marin ta ce cikin makonni masu zuwa kasar ta Finland za ta tantance matsayi kan shiga kungiyar ta NATO.
Kutsen da Rasha ta yi a Ukraine ya janyo muhawara kan shiga kungiyar NATO a kasashen na Finaland da Sweden, kana akwai gagarumin goyon bayan shiga kungiyar tsaron ta NATO a Finland, tun bayan kusten na Rasha a Ukraine.
A baya Finland ba ta shiga kungiyar NATO ba, saboda neman samun kekkyawar dangantaka da kasar Rasha, amma yakin da ke faruwa a Ukraine ya sauya komai.