Felix Tshisekedi ya ce Ruwanda mai laifi ce

Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, ya bayyana hakan ne yayin taron tsaro da ke gudana a yanzu haka a birnin Munich na Jamus. A cewarsa, babbar mai laifin da ya kamata a dauki mataki a kanta ita ce Ruwanda. Kalaman na Shugaba Tshisekedi na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Ruwandan da a wana Janairun da ya gabata ta kwace iko da birnin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon, ke kutsa kai kudancin kasar zuwa Bukavu babban birnin gundumar Kivu.


News Source:   DW (dw.com)