Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta yi watsi da kudirin hana bakin haure shiga kasar mai cike da cece-kuce wanda jam'iyyar CDU mai matsakaicin ra'ayin mazan jiya ta gabatar kuma ya samu goyon bayan jam'iyyar AfD mai kyamar baki. Sai dai da karamar rinjaye kudirin ya gaza wucewa, inda masu adawa da dokar wadda za ta tabbatar da hana bakin haure shiga kasar suka kada kuri'a 350, sannan masu goyon bayan kudirin dokar 338, kana 'yan majalisa biyar sun kaurace wajen kada kuri'a.
Karin Bayani: Jamus: Kudirin tsaurara dokar shige da fice
Duk da yadda wasu jam'iyyu suka yi alkawarin goyon bayan ayar dokar sakamakon ya nuna yadda 'yan majalisar daga wasu jam'iyyu suka gaza mutunta alkawarin da jam'iyunsu suka dauka.
Alice Weidel shugabar jam'iyyar AfD mai kyamar baki ta ce rashin nasarar amincewa da wannan dokar abin takaici ne, kuma haka ya nuna Friedrich Merz shugaban jam'iyyar CDU ya gaza shawo kan galibin 'yan majalisa wajen amince da dokar dakile bakin haure masu shiga Jamus. Idan da kudirin ya wuce kamar yadda aka zata, da Jamus za ta karfafa matakan hana bakin haure shiga kasar wajen karfafa tsaro a kan iyakokin kasar.