Shugaban sashin bayar da agaji na yankin gabashin Indonesiya, Avi Mangota Hallan ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran Jamus cewa, masu aiki ceto na ci gaba da neman wadanda ake tunanin baraguzan gidajen da suka kone sanadiyar fashewar dutse mai aman wutar ya danne su. Gwamnatin Indonesiya ta sanya dokar ta baci a yankunan da hatsarin ya shafa har zuwa ranar 31 ga watan Disambar 2024, kana an shawarci mazauna yankin da kuma masu yawon bude ido da su nisanci wurin da tsawo kilo mita bakwai.
Ko a farkon wannan shekarar, tsibirin na Flores ya fuskanci fashewar duwatsu masu aman wuta da dama, lamarin da ya tilasta kashe fiye da mazauna yankin dubu biyu.