Farautar masu rike da bindiga ba lasisi

Farautar masu rike da bindiga ba lasisi
'Yan sanda a yanki Soweto na kasar Afirka ta Kudu sun fara farautar mutanen da suka mallaki bindigogi ba da izini ba.

Wannan mataki dai na zuwa ne bayan jerin hare-hare da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai wasu mashaya da na baya-bayan nan ya hallaka akalla mutum 15.

Rike bindiga da mutane ke yi a kasar ba tare da lasisi ba na da nasaba da yawaitar hare-haren da kasar ke fuskanta musamman na 'yan kwanakin nan da aka kai gidan shan barasa sama da 4.

Sai dai har ya zuwa yanzu ba a san ko wadannan hare-haren na 'yan bindiga na da alaka da juna ba, amma al'umma a kasar na yada jita-jitan suna kama da na mayakan jihadi, kasancewar yadda ake ta haran gidajen shan giya,.

Kasar Afirka ta Kudu dai ta yi kaurin suna wajen manyan laifuka, inda ake alakanta su da talauci gami da rashin aikin yi da ya yi wa al'ummar kasar katutu, musamman ma a tsakanin matasa.


News Source:   DW (dw.com)