Farashin abinci ya haura

Farashin abinci ya haura
Farashin kayan abinci na ci gaba da tashi a sassan duniya lamarin da ke kara jefa marasa karfin cikin talauci.

Farashin kayayyakin abinci na ci gaba da tashi a daukacin sassan duniya cikin wannan shekara lamarin da yake da nasaba da yakin da ke faruwa sakamakon kutsen da Rasha ta kaddamar kan kasar Ukraine. Kasashen biyu suna kan gaba a duniya wajen fitar da alkama da takin zamani.

Wannan ya zo lokaci da wasu sassan duniya ke fuskantar matsalolin fari, da ambaliyar ruwa, da dumamar yanayi sakamakon sauyin yanayi da duniya take fuskanta.

Muddun tashin farashin kayan abincin ya ci gaba da tashi haka zai fi illa a kasashe matalauta musamman wadanda suke cikin tashe-tashen hankula kamar Afghanistan, Yemen, Sudan ta Kudu, da Syria.

 


News Source:   DW (dw.com)