Ofishin da ke da alhakin hana cin zarafin kananan yara a Faransa, ya bayar da sammacin kame Durov a wani bincike na farko kan laifukan zamba da safarar muggan kwayoyi da cin zarafi ta yanar gizo da manyan laifuka da inganta ayyukan ta'addanci.
Ana zargin Durov da rashin daukar matakan hana amfani da manhajar wajen yada manyan laifuka. Telegram ya yi alkawarin ba zai taba bayyana bayanai game da masu amfani da Telegram ba.
Kamfanin Telegram mai cibiya a Dubai, mamallakin sa Durov ya yi hijira daga kasarta ta asali wato Rasha a shekarar 2014 bayan da ya ki amsa bukatar gwamnati na rufe shafukan 'yan adawa a wani shafinsa mai suna VK wanda ya sayar daga baya.
Gwamnatin Rasha ta zargi Faransa da rashin ba da hadin kai ta gana da matashin dan kasarta mai shekaru 39, tana mai cewa wajibi a bayyana gamasassun hujjojin tsare shi.
Durov, wanda mujallar Forbes ta kiyasta yana da arzikin da ya kai dala biliyan 15 da rabi, ya ce a watan Afrilu wasu kasashe sun matsa masa lamba kan yadda manhajar za ta kasance amma ya ce, "manhajar yakamata ta kasance 'yar ba ruwantai" ba wai ta taka rawa "a siyasar duniya ba".
Elon Musk Mai shafin X, ya bukaci a saki a saki Pavel, kamar yadda ya wallafa a shafin , haka shi ma Tsohon dan takarar shugabancin Amirka Robert F. Kennedy Jr ya ce, a sakar wa 'yancin fadin albarkacin baki mara.