Faransa ta gargadi shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump bisa barazana ga iyakokin Tarayyar Turai bayan kalaman mista Trump kan amfani da soji wajen kwace Greenland.
Greenland yanki ne da ke karkashin kasar Denmark wacce ta kasance mamba a kungiyar Tarayyar Turai kuma tuni kalaman na Trump suka fara tada kura.
Tattalin arzikin Faransa zai bunkasa
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya shaida wa gidan rediyon Faransa na France Inter radio cewa babu batun barin wata kasa a duk duniya koma wacce ce ta taba martabar iyakokin nahiyar Turai.
Ministan na harkokin waje ya ce Turai nahiya ce mai karfi kuma dole ne a kara karfafata ba kuma neman kawo rarrabuwa ba kamar yadda wasu ke neman haddasawa.
Kotun Faransa ta tabbatar da hukuncin Sarkozy
Har ila yau, Barrot ya ce yankin Greenland mallakin Turai ne kuma yanki ne da ke cin gashin kansa a karkashin kasar Denmark wacce ita kuma ke cikin kungiyar EU.
A wani taron manema labarai a ranar Talata Donald Trump ya ki kore batun yiwuwar amfani da soji wajen karbe Greenland wadda ya ce ya na so ya koma karkashin kulawar Amurka.