Faransa ta fara kwashe dakarun sojinta daga kasar Chadi, farawa da jiragen yaki biyu da ke birnin N'Djamena, kamar yadda rundunar sojin ta sanar, bayan da Chadin ta sanar da yanke alakar tsaro da ita makonni biyu da suka gabata.
Mai magana da yawun rundunar sojin Faransa Kanar Guillaume Vernet, ya ce har zuwa wannan lokaci ba su kai ga cimma yarjejeniyar tsare-tsaren kwashe sojojin ba, haka zalika ba su cimma matsayar ko za a bar wasu sojojin su ci gaba da zama a Chadin ba.
Karin bayani:Chadi ta soke yarjejeniyar tsaro da Faransa
Mai magana da yawun rundunar sojin Chadi Chanane Issakha Acheikh, ya tabbatar da ficewar jiragen yakin Faransa daga kasar, yana mai cewar za su rinka sanar da al'ummar kasa yadda dakarun sojin Faransa za su ci gaba da barin kasar, har zuwa kammala ficewarsu.
Karin bayani:Kasashe rainon Faransa na korar sojojinta
Dama can Faransa ta jima da kwashe sojojinta daga kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar, sakamakon sabanin da ya kunno kai a tsakaninsu a dalilin juyin mulkin da sojoji suka yi a kasashen na yammacin Afirka.