Hukumomin Faransa sun ce sun dakile yunkurin kai hare hare har sau uku a lokacin gasar wasannin Olympics na 2024 da aka kammala a birnin Paris. Babban mai gabatar da kara na Faransa ya sanar da haka.
Olivier Christen ya shaida wa gidan radiyon Farnceinfo a Faransa cewa an kama mutane biyar da ake zargi da yunkurin harin ta'addanci.
An kama mutanen ne cikin tsauraran matakan tsaro a lokacin da ake gudanar da wasannin
Hukumomin sun gudanar da samame gida gida har 936 ya zuwa yanzu a cikin wannan shekarar idan aka kwatanta da samame 153 da suka kai a bara.