Faransa ta ba da sammacin kama Bashar al-Assad

Binciken jami'an hukumar ya zargi Assad da halaka fararen hula ba gaira ba dalili ta hanyar kai musu hare-hare da makamai masu guba, wanda dakarun sojin kasar suka kai garin Ghouta da ke kusa da birnin Damascus a shekarar 2013 da ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwar jama'a, ko da yake rahoton kungiyoyin kare hakkin bil'adama ya nuna cewa mutanen da suka mutu sun haura dubu daya.

An kai irin wannan hari na guba a birnin Daraa a shekarar 2017. Tun a cikin shekarar 2023 ne Faransa ta fara ba da sammacin kamo Bashar al-Assad, wanda mayakan 'yan tawayen HTS suka kawar daga kan karagar mulki a cikin watan Disamban shekarar 2024 da ta gabata, inda ya arce zuwa birnin Moscow na Rasha don samun mafakar siyasa.


News Source:   DW (dw.com)