A sakamakon zagayen farko na zaben Faransa da ya gudana a yau, shugaban kasar Emmanuel Macron ne ya zo na daya da kaso 28.1 yayin da abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen ke biye mishi a yawan kuri’u kaso 23.3
Hakan na nufin za a fafata a tsakanin su a zagaye na biyu a ranar 24 na wannan watan da muke ciki, ana ganin wannan karawar da za su yi sai ta fi wacce suka yi a shekarar 2017 zafi.
Macron na neman wa'adi na biyu wanda babu wani shugaban kasar da ya yi nasarar hakan tun bayan Jacques Chirac kusan shekaru 20 da suka gabata
Duk wanda ya sami sama da kaso 50 shi ne zai jagoranci kasar a wani wa’adi na shekaru biyar.