Ziyarar ta Shugaba Emmanuel Macron da ke zaman shugaban Faransa da aka haifa bayan Aljeriya ta samu 'yancin kanta, na zuwa ne a daidai lokacin da Agiers din ke bikin cika shekaru 60 da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na Faransan. Macron din dai na fatan ziyarar tasa za ta kawo karshen zaman 'yan marina da suke yi, tare da kasar da Faransan ta raina da ke yankin arewacin Afirka. Yayin ziyarar tasa Macron da mai masaukinsa Shugaba Abdelmadjid Tebboune na Aljeriya, za su ziyarci wuraren tarihi da kaburburan mutane da suka halaka a yakin neman 'yancin kai na Aljeriyan da aka kammala sama da shekaru 130 da suka gabata.