Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya sanar a Jumma'ar nan cewa akwai sauran burbushin fata na ganin yunkurin samar da kasashe biyu a yankin ''Gabar Yamma da Kogin Jodan'' ya yi tasiri wurin shawo kan rikicin Isra'ila da Falasdinawa. Abbas ya fadi haka ne jim kadan bayan ganawarsa da Shugaba Joe Biden na Amirka, wanda ke ziyarar kwanaki hudu a yankin Gabas ta Tsakiya.
A jawabin da Shugaba Biden ya yi, ya ce shi ma ya gamsu cewa Falasdinawa sun cancanci samun kasarsu mai cin gashin kanta, yana mai cewa koda a yanzu yanayin zaman lumana bai kai wanda za a shata iyakokin kasashen biyu ba, Amirka za ta ci gaba da kokarin ganin ta samar da fahimtar juna a tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.