Tsananin fada tsakanin Kurdawan kasar Syria wato SDF dake samun goyon bayan Amurka, da kuma tsagin da ke samun goyon kasar Turkiyya, ya yi sanadiyyar mutuwar mayaka sama da dari daga bangarorin biyu a kasar Syria, kungiyar kare hakkin 'dan adam ta Syrian Observatory for Human Rights ta sanar ranar Lahadi.
Karin bayani:Siriya ta yi sulhu da kungiyoyi masu dauke da makamai
Kurdawan SDF sun rasa mayaka 85 a fadan, yayin da tsagin da ke samun marawar dakarun Turkiyya ya rasa mayaka 16, bayan shafe tsawon kwanaki biyun da suka gabata suna gwabzawa a arewacin Syria ta sama da ta kasa, ta hanyar amfani da jirage marasa matuka da sauran makaman yaki.
Turkiyya dai na kallon kurdawan a matsayin wani bangare na 'yan tawayen PKK da Turkiyyar ke yaki da su tun cikin shekarun 1980.
Karin bayani:Yan sandan Jamus far wa Kurdawa yan Iraqi masu safarar baki
Yanzu haka dai 'yan tawayen HTS masu samun goyon bayan Turkiyya ne ke rike da kasar Syria, bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad a farkon watan Disamban shekarar 2024 da ta gabata.