Shugabar hukumar gudanarwa tarayyar Turai Ursula Von der Leyen ta ce a babban taron kungiyar da ke tafe a ranakun 23 zuwa da 24 na wannan watan, kasashe mambobin kungiyar za su yi zama na musamman da ke cike da tarihi domin kammala nazarin shigar kasar Ukraine kungiyar ta EU.
Von der Leyen ta ce babban kalubale ne za su fuskanta, amma lokaci ya yi da su duba bukatun nasu dama lalubo hanyar magance su. Ta kara da cewar ta na fatan a karshen taron nasu da ma shekaru 20 da ke tafe za su yi alfahari da matakin da suka cimma.
A nashi bangaren jakadan Ukraine da ke Jamus Andrij Melnyk ya bukaci mahukuntan na Berlin da ma sauran kasashen da ke kungiyar EU da su duba halin da suke ciki wajen yanke hukunci da zai kawo karshen matsalolin da suke fuskanta na tsawon shekaru.
A gaba a wannan watan ne shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai kai ziyara a birnin Kiev domin ganawa da Shugaba Volodmyr Zelensky kafin taron kolin kungiyar da ke tafe.