EU za ta janye wa Syria takunkumin karya tattalin arziki

Faransa ta sanar da cewa kungiyar tarayyar Turai EU na aikin kokarin janye wa Syria takunkumen da ke kanta, bayan da 'yan tawayen HTS suka hambarar da gwamnatin kama-karya ta  Bashar al-Assad a cikin watan Disamban 2024.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ne ya bayyana hakan yayin taro a birnin Paris, inda ya ce tun a cikin watan Janairun da ya gabata shi da sauran takwarorinsa na EU suka amince da dage takunkumin karya tattalin arziki da ke kan Syria, domin bata damar tada komadarta, musamman a fannin makamashi.

Karin bayani:Faransa ta ba da sammacin kama Bashar al-Assad

Shi ma ministan harkokin wajen Syria Asaad al-Shaibani ya samu damar halartar taron tattauna batun a karon farko a hukumance a nahiyar Turai, bayan halartar taron tattalin arziki na duniya na birnin Davos a watan Janairun da ya gabata.

Sanarwar da fadar mulkin Faransa ta fitar ta ce nan gaba ne shugaban Emmanuel Macron zai gabatar da jawabi a taron, wanda ke samun wakilcin Amurka da Jamus da Burtaniya, sai tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya da kasashen yankin Gulf, har ma da Turkiyya.

Karin bayani:Za a sake bude filin jirgin saman birnin Damascus na Syria

Kasashen yamma na nuna damuwa kan alkiblar da sabon shugaban rikon kwaryar Syria zai jagoranci kasar a kai, musamman ma ta bangaren bai wa tsirarun kabilu da addinai da kuma mata 'yancin walwalwa.


News Source:   DW (dw.com)