EU ta sake kakaba takunkumi ga Rasha

Ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar Tarayyar Turan EU ne suka kafa dambar daukar sabon matakin kan Moscow a Litinin din da ta gabata, inda takunkumin zai shafi sojojin ruwa da mamallakan manyan jiragen ruwan dakon mai na Rashan. A cewarsu jiragen ruwan dakon kayan da safarar man fetur din, na tallafawa Rasha wajen kauce wa farashin man fetur din da Turai ta tsayar da kuma safarar hatsin Ukraine da aka sato. Da take maraba da sababon matakin takunkumin kan Moscow da ke zuwa a daidai lokacin da shugabn Amurka Donald Trump ke son kawo karshen yakin Rasha da Ukraine, shugabar Hukumar Tarayyar Turan EU Ursula von der Leyen ta bayyana cewa EU za ta ci gaba daukar tsauraran matakai a kan jiragen ruwan na Rasha.


News Source:   DW (dw.com)