EU ta mika shirin farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran

EU ta mika shirin farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran
Kungiyar Taryyar Turai ta mika daftarin karshe kan tattaunawar da ake yi na neman farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran da kasashen yamamcin duniya suka cimma a shekarar 2015.

Iran ta ce tana sake bitar shawarwarin da aka tsayar don ceto yarjejeniyar ta nukiliya aka cimma a 2015 da kasahen yammacin duniya, bayan da kungiyar Tarayyar Turai ta gabatar da kundin karshe na tattaunawar ceto yarjejeniyar a ranar Litinin.

A ranar Alhamis ce kasashen Biritaniya da Chaina da Faransa da Jamus da Iran da Rasha da kuma Amirka suka sake komawa teburin tattaunawa a Vienna, watanni bayan dakatar da batun.


News Source:   DW (dw.com)