EU ta fitar da makudan kudi domin tallafawa Ukraine

Shugabar Hukumar Tarayyar Turan Ursula von der Leyen ce ta wallafa hakan a shafinta na X, inda ta ce kudin za su taimaki Ukraine a harkokin gudanar da kasar a daidai lokacin da take ci gaba da gwabza fada da makwabciyarta Rasha.

Von der Leyen ta kara jaddada cewa, Turai na tsaye kyam tare da Ukraine. Wannan tallafi dai wani bangare ne na tsarin da suka amince da shi cikin watan Afrilun wannan shekara, wanda a karkashinsa Kyiv din za ta samu tallafin da yawansa ya kai kimanin Euro biliyan 50 nan da shekara ta 2027.

 

 


News Source:   DW (dw.com)