Kungiyar tarayyar Turai EU ta shiya sanar da Isra'ila cewa wajibi ne a mayar da al'ummar yankin Gaza gidajensu na asali cikin mutuntawa, kuma za ta bayar da gudunmawa don sake gina mu su muhallansu da yaki ya ragargaza, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi tozali da takardun bayanan.
Karin bayani:Hamas ta amince da sakin Isra'ilawa 3 da ta yi garkuwa da su
Wannan ra'ayi na EU ya yi kamanceceniya da na kasashen Larabawa, wanda kuma ya ci karo da muradin shugaban Amurka Donald Trump da ke ikirarin kwace yankin Gaza don sake gina shi, da nufin mayar da al'ummar zirin zuwa wasu kasashen.
Karin bayani:Trump ya bai wa Hamas wa'adin sakin Isra'ilawa da ke Gaza
EU wadda ke kan gaba wajen taimakawa Falasdinawa, za ta bayyana matakin nata ne a taron birnin Brussels na ranar 24 ga wannan wata na Fabarairu da mu ke ciki.