Kungiyar tarayyar Turai ta bayyana damuwarta a game da ci gaba da farmakin da sojojin Isra'ila ke kaiwa a yankunan gabar yamma da kogin Jordan dake yankin Falasdinawa.
Kwanaki 40 da aka kwashe sojojin na IDF na kai hare-hare a yankin inda mafi akasari a sansanonin da Falasdiunawa ke samun mafaka ya yi sanadiyar rayukan fararen hula da dama.
Kungiyar ta EU ta yi kira ga mahukuntan Isra'ila da su kiyaye dokokin kasa da kasa ta hanyar kare fararen hula a yayin kai farmakinsu a yankunan.
Bugu da kari sanarwar ta EU ta kara da cewar akwai bukatar Isra'ila ta dauki mataki a kan yan share wuri zauna dake korar mutane daga gidajensu.
Rahotannin sun tabbatar da karuwar shingayen bincike a wannan yankin da Isra'ila ta mamaye a wani rikici na kwanaki shida a shekarar 1967.
Karin Bayani: Isra'ila ta kai farmaki gabar yamma