EU ta bukaci al'umar nahiyar su jure wahala

EU ta bukaci al'umar nahiyar su jure wahala
A daidai lokacin da ake cigaba da gwabza yaki tsakanin Rasha da Ukraine, al'ummar nahiyar Turai na fuskantar tsadar farashin makamashi da yayi karanci a Turai

Babban jami'in diflomasiyar Turai Josep Borrell, ya yi kira ga al'ummnar nahiyar da su kara jure wa matsalar tashin farashin makamashi da nahiyar ke fuskanta a halin yanzu bayan soma yakin Ukraine.

Mista Borrell na kalaman ne a yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen EU da ya gudana a Bejiyam inda ya ci gaba da cewa halin da ake ciki wata alama ce ta neman kara jajircewar kamfanonin nahiyar kan matakan da kasashen suka dauka.

"Bai kamata kamfanonin Turai su nuna gazawa ba, kamata ya yi kamfanoni da gwamnatocin Turai su jajirce don mutunta matakan da suka dauka."

Babban jami'in na harkokin wajen EU ya kuma kara da cewa Shugaba Putin na tsammanin ko 'yan dimukuradiyya na da rauni.


News Source:   DW (dw.com)