Jakadun kasashen Tarayyar Turai 27, sun yi wani zama na nemo hanyoyin warware wani tarnaki da suka samu a game da aniyarsu ta kara takunkumin karya tattalin arzikin Rasha karo na shida, mai alaka da dakatar da shigo da mai daga Moscow.
Tun da fari dai kasar Hungary ce ta toshe shirin kasashen na EU, kasar da ke da karfi ta fuskar zirga-zirgar jiragen da ke dakon man daga Rasha.
Faransa wacce ke shugabancin kungiyar EU a yanzu, ita ce ta gabatar da bukatar sake duba batun a wannan Lahadin ta yadda za su ci gaba da ganin sun ladabtar da Rasha saboda wutar yaki da kunna a Ukraine.
Kasar ta Hungary dai na dogaro ne da danyen man kasar Rasha da akalla kashi 65%, wanda ake aikawa ta bututun nan na Druzhba wanda ya fi kowanne girma a duniya.