Hukumar tarayyar Turai ta ce tana hasashen mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine zai kara tashin farashin kayayyaki zuwa kashi 7.6 cikin dari wanda aka dade ba a gani ba. Bugu da kari hukumar ta kuma yi hasashen za a sami tsaiko a cigaban tattalin arziki a 2022 da kuma 2023.
Tsadar kayayyaki a kasashe masu amfani da kudin euro ya yi matukar tashi saboda yakin Ukraine kamar yadda hukumar tarayyar Turan ta wallafa.
Mataimakin shugaban hukumar Turan Valdis Dombrovskis ya ce yakin Rasha a kan Ukraine na cigaba da dakushe hasken tattalin arziki a nahiyar Turai.
Yakin dai ya haifar da tashin gwauron zabi na farashin abinci da makamashi a Turai yayin da kasashe ke fafutukar lalubo hanyoyin da za su kauce wa takunkumin da aka sanya wa wasu muhimman kayayyaki.