A sanarwar da kungiyar ta EU mai mambobi 27 ta fitar a yau, akwai bukatar daukar tsauraran matakai a kokari na kawo karshen sinadarin carbon dioxide (CO2) da ke haddasa dumamar yanayi.
Wannan mataki dai na nufin sannu a hankali a duk wadannan kasashen za a dai na samar da motoci da ke amfani da man fetur da na diesel ya zuwa motoci masu amfani da lantarki da kuma batura.
Shirin da ke da nufin nan da shekarar 2050 a samar da kyakyawar iska da bata dauke da sinadari carbon a ciki a daukacin nahiyar.
Ana ganin wannan mataki da mahukuntan na EU suka yanke shawarar dauka zai samar da mumunan koma baya ga kamfanonin da ke samar da motoci.