Erdogan ba ya maraba da Filland da Sweden

Erdogan ba ya maraba da Filland da Sweden
Shugaban kasar Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, ba su cimma matsaya ba a tattaunawarsu da wakilan kasashen Filland da Sweden da ke son shiga kungiyar tsaro ta NATO.

Shugaba Racep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, tattaunawar tasu ta makon da ya gabata ba ta cimma fatan da ake da shi ba. A cewar Erdogan Ankara ba za ta goyawa kasashen da take zargi da marawa 'yan ta'adda baya su shiga cikin kungiyar tsaron ta NATO ba, kamar yadda kafar yada labaran kasar TRT ta ruwaito. Turkiyya dai ta yi watsi da bukatar kasashen na Filland da Sweden din ta shiga NATO, inda aka ruwaito Erdogan na cewa ba su da gaskiya a wata hira da ya yi da manema labarai bayan dawowarsa daga wata ziyarar aiki da ya kai Azerbaijan.


News Source:   DW (dw.com)