Equatorial Guinea ta kori alkalin alkalai

Equatorial Guinea ta kori alkalin alkalai
Hukumomin kasar da ke mulki tamkar na gado ba su nuna alamun hukunta jami'in ba. 'Da ga shugaban kasar ne mataimakin shugaban kasa. Shi da kansa ya fara bankado badakalar cin hancin ta babban jami'in shari'ar kasar.

Shugaban kasar  Equatorial Guinea  Teodor Mbasogo ya kori alkalin alkalan kasar David Eyang bayan da babban jami'in ya amince da laifinsa na karbar cin hanci domin yin rufa-rufa a wasu kayan abinci da magungunan da wani kamfani ke sayar wa 'yan kasar duk da cewa wa'adin da aka rubuta a jikinsu ya wuce. 

A sanarwar da shugaban da ya kwashe shekaru 43 yana mulkin kasar Equatorial Guinea mai arzikin man fetur a tsakiyar Afirka ya fitar a ranar Asabar ya ce alkalin alkalan kasar ya yi sakaci da ayyukansa. 


News Source:   DW (dw.com)