ECOWAS: Taro kan yawan juyin mulki

ECOWAS: Taro kan yawan juyin mulki
Watanni bayan takun saka tsakanin ECOWAS da sojojin da suka kifar da gwamnati a Burkina Faso da Gini da Mali, shugabannin kasashen kungiyar na taron koli don daukar mataki

Shugabannin kasashen yankin yammacin Afirka na halartar taron koli na kungiyar ECOWAS a wannan Asabar a birnin Accra na kasar Ghana da nufin duba matakan da za su dauka wa sojojin da suka yi juye-juyen mulki a wasu kasashen yankin.

Kasashen Burkina da Gini da Mali ne ke kan gaba daga muhimman batutuwan da za su dauki hankali a taron da ma batun duba yiwuwar sake mika ragamar mulki ga gwamnatocin fafrar hula bayan da sojoji suka yi wa tafarkin dimukuradiyya hawan kawara.

Fadar gwamnatin Bamako daya daga cikin kasashen da ke takon saka da kungiyar, ta ambaci shirinta na sake mika mulki nan da watanni 24 masu zuwa, matakin da ECOWAS ta yi fatali da shi.

Ko baya ga batun juyin mulki a kasashen, batun tsaro na daga cikin wasu muhimman batutuwan da za su dauki hanakali duba da yadda harkokin tsaron ke kara sukurkucewa a yankin.


News Source:   DW (dw.com)