Dusar kankara ta ruftawa wasu mutane a Himalaya na Indiya

Ministan Indiya da ke kula da jihar Uttarakhand, Pushkar Singh Dhami, ya ce masu aikin ceton na gudanar da aiki tukuru wajen ganin sun lalubo mutanen da ran su.

Karin bayani: Girgizar kasa mai karfi ta afku a yankin Himalaya na Tibet

Tun da fari dai 'yan sanda sun bayyana cewa mutane 55 ne dusar kankarar ta ruftawa a yankin kuma a halin yanzu jami'an kiwon lafiya na ci gaba da duba wadanda suka ji raunuka. Ma'aikatan dai na gudanar da aiki a yankin Chamoli da ke kan iyakar Indiya da Tibet.

Karin bayani: Wasu sun mutu a hawa tsaunin Himalaya

A shekara ta 2021, kimanin mutane 100 ne suka mutu a yankin na Himalayan da ke jihar ta Uttarakhand sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da kuma zafatarewar kasa. Kazalika a 2023 wasu mutanen kimanin 6,000 suka mutu duk dai a yankin da ke fama da kalubale na sauyin yanayi.


News Source:   DW (dw.com)