Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa mutane sama da miliyan bakwai ke bukatar daukin gaggawa a jihohi uku da ke shiyyar da suka hadar da Adamawa da Borno da kuma Yobe, duk da cewa MDD ta ce mutum miliyan 3.6 za ta iya bai wa tallafi daga cikin adadin.
Karin bayani: MDD ta yi gargadi kan baraznar yunwa a arewacin Najeriya
Gabanin wannan ratoho da Reuters ta gani, majalisar ta ce kasashe sun manta da halin da ake ciki a Arewa maso gabashin Najeriya kasancewar hankalin duniya ya karkata kan Ukraine da Gaza da kuma Sudan.
Karin bayani: Mayakan ISWAP sun halaka manoma sama da 40 a jihar Borno da ke Najeriya
Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na ganin cewa manufofin Shugaba Bola Ahmad Tinubu kan tattalin arziki shi ne ummul-aba'isin jefa 'yan kasar cikin yanayi na damuwa da tsadar rayuwa, sai dai gwamnatin APC ta ce matakin shi ne mafita.