Kudaden da duniya ke kashewa kan sojoji da samar da makamai sun kusan Euro tiriliyan biyu a karon farko a tarihin duniya. Cibiyar bincike kan zaman lafiya ta duniya, SIPRI, a cikin rahoton da ta fitar a wannan Litinin ta ce an kashe wadannan kudade ne a shekarar da ta gabata kadai. Kudaden sun haura abin da duniya ta kashe a shekara ta 2012 a kan harkokin soji da sama da kaso 12 cikin 100.
Wani babban jami'i a cibiyar ta SIPRI Diego Lopes da Silva ya ce duk da yadda tattalin arzikin duniya ya samu tawaya sakamakon zuwan corona, kasashe dabam-dabam sun kara azama wurin kimtsa rundunoninsu na soji.