Masu aikin ceto sun yi nasarar kubutar da mutane 27 daga cikin sama da 80 da ke makare a cikin kwale-kwalen, yayin da ake ci gaba da neman wasu mutanen kimanin 48 a gabar tsibirin El Hierro.
Karin bayani: Spain ta ceto 'yan ci-rani 516 daga Afirka a tsibirin Canary
Hukumar kula da 'yan gudun hijra na Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta ce sama da mutum 30,000 suka isa tsibirin na Canary a iya wannan shekarar ta 2024. Hukumar kididdigar 'yan gudun hijra ta Spain ta ce mutane sama da 4,800 sun nutse a ruwa daga watan Janairu zuwa Mayu.