DR Kwango ta tabbatar da kasancewar sojojin Ruwanda a Goma

Gwamnatin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta tabbatar da kasancewar sojojin kasar Ruwanda a Goma, bayan da 'yan tawayen M23 suka kwace birnin. Kakakin gwamnatin Kwango Patrick Muyaya ya ce dakarunsa na fafutukar kare kai daga kashe-kashe, yayin da daya hannun, ya yi kira ga mazauna Goma da su ci gaba da zama a gidajensu tare da guje wa lalata da dukiya da kwasar ganima.

Karin bayani: Rikicin Jamhuriyar Kwango da Ruwanda ya yi kamari

Al'amura na ci gaba da tabarbarewa a birnin Goma tun bayan 'yan tawayen na M23 suka shiga tsakiyar birnin, inda dubban fursunoni suka tsere daga gidan yari. Shi kuwa Kakakin rundunar sojin Ruwanda Ronald Rwivanga, ya ce an kashe 'yan kasarsa biyar, yayin da wasu 25 suka samu raunuka bayan da sojojin Kwango suka harba makamai a yankin Gisenyi da ke kan iyakar kasashen biyu.

Karin bayani: 'Yan tawayen M23 sun yi ikirarin kwace birnin Goma da ke gabashin Kwango

Kasashen duniya na ci gaba da neman hanyar warware rikici a tsakanin Kwango da Ruwanda, inda ake sa ran gudanar da taron shugabannin kasashen gabashin Afirka a ranar Laraba, yayin da a gobe Kungiyar Tarayyar Afirka za ta yi taro domin tattauna rikicin gabashin kasar.

 


News Source:   DW (dw.com)