Lourenço da ke yin ziyara a Portugal ya ce ya tura ministan harkokin wajensa domin duba lafiyarsa. An kwantar da tsohon shugaban Kasar Angola José Eduardo dos Santos mai shekaru 79 a duniya a wani asibiti da ke gabashin Kasar Spain a makon da ya gabata bayan da aka ce yanayin lafiyarsa ya tabarbare. Likitiocin asibitin dai sun ki su yi bayyani a kan rashin lafiyarsa a game da abin da ke damunsa. An zargi dos Santos da yin almubazzaranci da dukiyar kasa ta hanyar fifita iyalansa da kuma masoyansa. Ya mulki Angola a tsawon shekaru 38, har sai da shugaban kasar na yanzu Joao Lourenço ya gaje shi a shekara ta 2017.