Donald Trump zai kara haraji kan China da Mexico da Kanada

Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya ce da zarar ya shiga fadar White House zai sanar da karin harajin fiton kayayyakin kasashen Mexico da Kanada da kuma China da ke shiga kasar, har sai sun dakile hanyoyin safarar miyagun kwayoyi cikin Amurka.

Karin bayani:Kasar China ta ce za ta yi aiki ga gwamnatin Trump

Mr Trump ya ce zai kara wa Mexico da Kanada harajin kashi 25 cikin 100, yayin da ita kuma China zai kara mata harajin kashi 10 cikin 100, a ranar farko ta kama aiki, wato 20 ga watan Janairun sabuwar shekara mai kamawa ta 2025, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social.

Karin bayani:Amurka ta bukaci Rasha da Ukraine zama a teburin sulhu

Jim kadan da fitar wannan sanarwa kuma sai China ta mayar da martanin cewa cacar baka a fagen kasuwanci ba ta haifar da alheri ga kowane bangare, kamar yadda mai magana da yawun ofishin jakadancin China a Amurka Liu Pengyu ya wallafa a shafinsa na X.


News Source:   DW (dw.com)