Zababben shugaba Donald Trump karkashin tsarin jam'iyyarsa ta Republican na da niyyan sake fasalin tsarin lamuran kasar da ma dangantakarta da wasu kasashe.
Ana sa ran Trump zai dauki matakin gaggawa bayan bikin rantsuwar, na rattaba hannu kan wasu batutuwa da aka riga aka tsara da suka hadar da korara baki marasa takardu zaman Amurka, da rage kariyar ma'aikatan gwamnati, bisa alkawarin cewa wa'adinsa zai kawo sabon yaanayi a tsarin rayuwar Amurka da wadata da mutunci daura da alfahari.
Yanayi na tsananin sanyi ya sa an mayar da bikin rantsar daTrump a cikin harabar majalisar kasar a karo na farkon faruwar irinsa a cikin shekaru 40, an maye gurbin faretin bukin da wani taron da za a yi a filin wasa na cikin gari.