Sabon zababben shugaban Amurka Donald Trump na ci gaba da bayyana sunayen mutanen da ake ganin za su kasance mambobi a gwamnatinsa idan ya karbi rantsuwar kama aiki a farkon watan Janairu na sabuwar shekara.
Karin Bayani : Afirka na fatan samu kulawa daga Donald Trump
Jardiar New York Times ta ambato yiwuwar Shugaba Trump ya nada Sanata Marco Rubio a matsayin babban sakataren harkokin wajen kasar Amurka a karkashin mulkinsa.
Marco Rubio mai shekaru 53 na daya daga cikin 'yan takarar da suka bayyana anniyar yi rike wa Donald Trump gargada a zaben da ya lashe a matsayin mataimaki a yayin zaben fidda gwani na jam'iyyar Republican.
Karin Bayani : Donald Trump ya sanar da wanda zai kori bakin haure daga Amurka
Sabon shugaban na Amurka Donald Trump ya zabi Elise Stefanik wata mai rajin kare manufofin Trump a matsayin sabuwar jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, matakin da tuni ya dadawa Isra'ila.