A wannan Litinin din ce birnin Davos ma kasar switzerland ke karbar bakoncin taron tattalin arzikin duniya na shekara shekara a karo na 55 mai taken "Hadin kai don zamnin fasaha".
Taron na bana dai ya zo ne a daidai lokacin da ake gudanar da manyan zabuka a kasashe da dama da aka kori masu rike da madafun iko da dama, kazalika da rantsar da Donald Trump da ya sake lashe zaben Amurka kuma ke da manufofin da ke barazana ga harkokin cinikayya.
Karuwar masu ra'ayin rikau da yakin Ukraine da yanayin ayyukan jin kai a Gaza bayan yakin watanni 15, da ma tsananta yanayi na yau da kullum sakamakon sauyin yanayi zuwa yunkowar fasahar kirkira ko kuma AI, sun kasance wasu daga cikin mahimman batutuwan da wakilai daga kasashe sama da 130, za su tattauna a zauren taron na yini biyar.
Shugaban taron tattalin arzikin na duniya Borge Brende ya shaida wa manema labarai cewa, taron na wakana ne a mafi rikitaccen yanayin siyasar kasa da kasa.
Kusan shugabanni 3,000, da suka kunshi shugabannin kasashe da gwamnatoci 60, daga kasashe sama da 130 ake sa ran halartar taron tattalin arzikin na bana abirnin Davos na kasar Switzerland ciki har da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da da shugabar hukumar Taraiyar Turai Ursula von der Leyen.