Daukar tsoffin 'yan tawaye aikin soja

Daukar tsoffin 'yan tawaye aikin soja
Shekaru bayan kasa tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan tawaye, gwamnatin Mali za ta daukar tsoffin mayakan 'yan tawayen arewacin kasar aikin soja.

Gwamnatin rikon kwarya ta mulkin soja a Mali ta cimma matsaya ta shimfida zaman lafiya da mayakan 'yan tawayen Abzinawa da ke arewacin kasar, inda za ta ba wa mutane dubu 26 daga cikin mayakan a guraben aiki.

Fadar mulki ta birnin Bamako ta ce za a dauki mutun dubu 13 a zangon farko na aiwatar da yarjejeniyar, kana bayan ba su horon sanin makamar aikin soja za su koma a yankunan arewacin kasar don kara tabbatar tsaro kan nan zuwa shekarar 2024.

A shwekarar 2015 ne dai gwamnatin Mali ta kulla yarjejeniyar zaman lafiya a binrin Alger da 'yan awaren na Abzinawa masu ikrarin kafa kasar Azawak a arrwacin Mali, sai dai an fuskanci tarnaki a gabanin soma amfani da yarjejeniyar tun bayan da aka kifar da gwamnatin farar hula a kasar watanni da dama da suka gabata.


News Source:   DW (dw.com)